<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>180</hymn_number>
<title>A Cikin Yesu Na Sami Rai, A Cikinsa Kaɗai LW180</title>
<lyrics>[V1]
 1) A cikin Yesu na sami rai, a cikinsa kaɗai,
 Salama kuwa da kwanciyar rai, murna ba fasawa.

[V2]
 KORUS
 Yesu shi ne Mai Cetona, ba wani wanda na fi so.
 Salama, murna, kwanciyar rai, sai cikin Almasihu.

[V3]
 2) Raina bai sami hutu ba a cikin duniyan nan,
 Amma ƙaunar Mai Cetona ta hutasshe ni nandanan.
 Korus

[V4]
 3) Dā mutane suka kashe shi, amma ya tashi kuwa.
 Shi kuma za ya dawo nan, zai karƃi mulkinsa.
 Korus

[V5]
 4) Mai zuwa ba ya korarsa, mai tuba kuwa ba ya ƙi.
 Kuma mai ba da gaskiya, Yesu zai cece shi.
 Korus</lyrics>
</song>